30 Afirilu 2026 - 22:20
Source: ABNA24
Hizbullahi Na Ci Gaba Da Martani Kan Sojojin Isra'ila + Bidiyo

Kafofin yada labaran gwamnatin sahyoniyawan sun ba da rahoton mutuwar sojojin sahayoniya biyu a kudancin Lebanon bayan hare-haren da jiragen Hizbullah ta kai. 

Kamfanin Dillancin Labaran ƙasa da ƙasa na Ahlul-Baiti (ABNA) ya habarta cewa: Hizbullahi ta fitar da bidiyon lokacin da ta kai hari kan sojojin Isra'ila da ke dauke da makamai tare da jirgin maras matuki a kudancin Lebanon. Sannan Kungiyar Hizbullah ta kasar Lebanon ta sanar da cewa ta harbo wani jirgin sama mara matuki nau'in Hirmus 900 a sararin samaniyar garin Al-Qantara da ke kudancin Lebanon da makami mai linzami. 

Sannan Hizbullah a martaninta ga laifukan sahyoniyawa ta kakkaɓo wani jirgi mara matuki. Kamar yadda Kungiyar Hizbullah ta kasar Labanon ta sanar, ta harbo wani jirgin sama mara matuki nau'in Hirmus 450 da makami mai linzami zuwa sama a sararin samaniyar Al-Natya. A wata sanarwar kuma, kungiyar ta ce ta kai hari tare da lalata makaman Isra'ila a kudancin garin Yarin ta hanyar amfani da wani jirgin sama maras matuki. 

Tashar Isra'ila ta 15: Hizbullah ta yi amfani da wani jirgin sama mara matuki na fiber optic a karon farko a safiyar yau a hare-haren da ta kai kan Al-Jalil, lamarin da ya kai ga fashewa tare da tarwatsewar wata motar sulke.

Your Comment

You are replying to: .
captcha